EFCC ta shawarci a dakatar da wasu manyan jami'an gwamnati don bincike - Magu

EFCC ta shawarci a dakatar da wasu manyan jami'an gwamnati don bincike - Magu

Shugaban hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance, mallakin gwamnatin tarayya mai suna Ibrahim Magu ya bayyana cewa shi da kansa ya shawarci a kori manyan daraktocin hukumar nan ta NEMA da aka samu da laifin badakalar kudi.

A cewar sa, tun a watan Disembar bara ne dai hukumar ta sa ta samu wata takardar korafi akan wadanda ake zargin inda bayan sun bincika kuma suka tabbatar da aikata laifukan na su sannan kuma suka shawarci a dakatar da su har sai an kammala bincike.

EFCC ta shawarci a dakatar da wasu manyan jami'an gwamnati don bincike - Magu

EFCC ta shawarci a dakatar da wasu manyan jami'an gwamnati don bincike - Magu

KU KARANTA: PDP na cigaba da zawarcin Sanata Shehu Sani

A wani labarin kuma, Wata babbar kotu dake a unguwar Maitama a garin Abuja, babban birnin tarayya ta bayar da umurmi ga jami'an tsaron Najeriya da suka hada da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron farin kaya watau SSS da kar su kuskura su kama Satana Ovie Omo-Agege daga jihar Delta.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya biyo bayan bukatar Lauyan Sanatan mai suna Aliyu Umar ya roki kotun a cikin karar da ya shigar a gaban ta .

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel