'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba sun farwa wani babban jigon jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress ta jihar Edo dake a shiyyar kudu maso kudancin kasar nan, mai suna Mista Samson Sedi a karamar hukumarEtsako ta yamma.

Haka zalika kamar dai yadda muka samu, kwamishinan 'yan sandan jihar ta Edo Mista Johnson Kokumo ma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mamacin ya mutu ne bayan an garzaya da shi asibiti.

'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

Legit.ng ta samu cewa sai dai Mista Johnson Kokumo ya kara jaddada cewa tuni jami'an sa suka dukufa wajen ganin sun cafke wanda yayi ta'asar.

A wani labarin kuma, Wata babbar kotu dake a unguwar Maitama a garin Abuja, babban birnin tarayya ta bayar da umurmi ga jami'an tsaron Najeriya da suka hada da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron farin kaya watau SSS da kar su kuskura su kama Satana Ovie Omo-Agege daga jihar Delta.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya biyo bayan bukatar Lauyan Sanatan mai suna Aliyu Umar ya roki kotun a cikin karar da ya shigar a gaban ta .

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel