Canji: Za'a fara kera motoci masu anfani da iskar gas a Najeriya

Canji: Za'a fara kera motoci masu anfani da iskar gas a Najeriya

Wani kamfanin kere-kere a Najeriya mai suna Power Gas ya shiga yarjejeniyar kasuwanci tare da kulla alaka da takwaran sa na kasar Austria domin fara kera motocin da ke anfani da iskar gas ba man fetur ba a Najeriya.

Kamar dai yadda kamfanin ya bayyana shirin na su zai fara karkata ne ga sauya fasali tare da samfurin motocin hayar da ake anfani da su a garuwan Legas da ma wasu dake a shiyyar kudu-maso-kudancin kasar.

Canji: Za'a fara kera motoci masu anfani da iskar gas a Najeriya

Canji: Za'a fara kera motoci masu anfani da iskar gas a Najeriya

KU KARANTA: Dan shekara 108 ya fadi sirrin tsawon rayuwa

Legit.ng ta samu cewa kamfanin haka zalika ya bayyana cewa idan har hakan ta tabbata, to tabbas kasar za ta ci ribar kimanin dalar Amurka biliyan 2.5 duk shekara sakamakon rage anfani da man fetur din da hakan zai haifar.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tab batar mana da cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai farashin gangar danyen mai ya yi tashin gwauron zabo a kasuwannin duniya da bai taba yi ba tun shekarar 2014.

Kamar dai yadda muka samu, yanzu dai ana sayar da gangar danyen man ne a kasuwar duniya akan farashin Dalar Amurka 74.44, farashin da bai taba kaiwa ba kusan shekaru hutu kenan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel