Fayose, Obanikoro da Omisore sun yi asarar dukiya ta N2.273b ga hukumar EFCC

Fayose, Obanikoro da Omisore sun yi asarar dukiya ta N2.273b ga hukumar EFCC

Hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta Najeriya watau EFCC, ta samu nasarar yakice wata dukiya ta kimanin N2.273 b daga hannun gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore da kuma tsohon karamin ministan tsaro, Sanata Musuliu Obanikoro.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wannan adadin kudi da hukumar EFCC ta yakito yana daga cikin N4.685b da ofishin mai bayar da shawara akan harkokin tsaro na kasa ya ware masu.

Wannan kudi dai wani bagire daga cikin $2.1b na kudin makamai da suka salwanta a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda Fayose da Omisore suka samu nasu kason domin yakin neman zaben kujerar gwamna ta jam'iyyar PDP a shekarar 2014.

Fayose, Obanikoro da Omisore sun yi asarar dukiya ta N2.273b ga hukumar EFCC

Fayose, Obanikoro da Omisore sun yi asarar dukiya ta N2.273b ga hukumar EFCC

Rahotanni sun bayyana cewa, cikin kowane lokaci a halin yanzu ana iya fara gudanar da shari'a akan Omisore sakamakon tuhuma gami da zargin da hukumar EFCC take a kansa.

KARANTA KUMA: Hukumar Kwastam ta datse kayan Fasakauri na kimanin N65m a jihar Kaduna

Sai dai gurfanar da Fayose a halin yanzu ba zai tabbatu sakamakon shinge da kujerar sa ta gwamna ke yi masa, inda da zarar ya kammala wa'adin zai fuskanci na shi hukuncin.

Jaridar Legit.ng ta kuma samu cewa, hukumar ta EFCC na ci gaba da gudanar binciken ta akan tsohon minista Obanikoro a sakamakon wasu zargi daban-daban da jami'an tsaro ke yi a kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel