Da dumin sa: Kocin kungiyar Arsenal ya sanar da lokacin da zai yi murabus

Da dumin sa: Kocin kungiyar Arsenal ya sanar da lokacin da zai yi murabus

Jami'in da ke horas da 'yan kwallon kungiyar nan ta Arsenal dake birnin Landan, mai suna Arsene Wenger daga karshe dai ya amince da yayi murabus daga mukamin sa da ya shafe kusan shekaru 22 yana a kai a karshen kakar wasannin bana.

Da dumin sa: Kocin kungiyar Arsenal ya sanar da lokacin da zai yi murabus

Da dumin sa: Kocin kungiyar Arsenal ya sanar da lokacin da zai yi murabus

KU KARANTA: An gano alakar Buhari da babban Bishof din Ingila

Arsene Wenger din dai ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai inda a cikin ta kuma ya yabawa dukkan 'yan wasan kungiyar, magoya bayan ta da kuma dukkan shugabannin kungiyar a dukkan matakai bisa goyon bayan da yace sun bashi.

Legit.ng dai ta samu cewa haka zalika masu sharhi akan al'amurran yau da kullum a harkokin wasanni sun bayyana cewa wannan dai wani abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba duk don nan kusa saboda tarihin ta.

A baya dai mai horas da 'yan wasan ya sa suka daga dumbin magoya bayan kungiyar da suka kallon baya tabuka komai kuma yana jawowa kungiyar koma-baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel