An saka ladan N500,000 a kan 'yan bindiga da suka kashe dan sanda a caji ofis

An saka ladan N500,000 a kan 'yan bindiga da suka kashe dan sanda a caji ofis

- Wasu 'yan bindiga sunkai hari ofishin yan sanda inda suka kashe dan sanda daya suka tafi da bindigarsa

- Hukumar Yan sanda reshen jihar Neja tayi alkawarin bayar da N500,000 ga wanda ya taimaka aka kamo maharan

- Kwamishin Yan sandan jihar kuma ya kafa kwamitin mutane bakwai don gundanar da bincike kan harin

A ranar Alhamis ne hukumar yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa wasu 'yan bindiga sunkai musu hari a ofishinsu na Kutigi dake karamar hukumar Lavun. Inda suka kashe Saja Jibril Abubakar kuma suka dauke bindigarsa.

Kisan Dan sanda a Neja: Za'a a bayar da N500,000 ga duk wanda ya taimaka aka gano wanda yayi kisan

Kisan Dan sanda a Neja: Za'a a bayar da N500,000 ga duk wanda ya taimaka aka gano wanda yayi kisan

DUBA WANNAN: An gano sunan dalibar da suka yi waya da Farfesa mai rabon maki bayan lalata

Mai magana da yawun hukumar, ASP Muhammadu Abubakar ya bayyanawa manema labarai cewa maharan sunkai harin ne da misalin 3:50 ma dare, yayin da suka bude wuta ga ma'aikatan dake kan aiki kuma suka sami nasarar korar su.

Me maganar yawun hukumar yace kwamishinan yan sandan, Dibal Yakadi ya kafa kwamiti na mutum bakwai wanda ASP Abdullahi Tahir zai jagoranta domin binciko wanda suka kai harin.

Yace akwai alkawarin 500,000 ga duk wanda yayi nasarar bayar wasu bayanai daza a iya amfani dashi don kama wanda suka kai harin.

Hukumar kuma tayi kira ga mazauna garin da su taimaka da bayyanai masu amfani ta yadda 'yan sandan zasu gano miyagun kuma su cigaba da tabbatar da zaman lafiya a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel