Ba bu wani tallafi na agaji da Hukumar NEMA ta bamu - Geidam

Ba bu wani tallafi na agaji da Hukumar NEMA ta bamu - Geidam

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam ya yi tonon silili inda bayyana cewa, ba bu wani tallafi na agaji da hukumar NEMA ta baiwa jihar sa duk da kasancewar ta daya daga cikin jihohi masu fama da rikicin ta'addanci.

Gwamnan ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya aikawa kwamitin majalisar wakilai akan harkokin bayar da agaji na gaggawa da sanadin kwamishinan ilimi na jihar sa, Ibrahim Lamin.

Gwamnan jihar Yobe; Ibrahim Geidam

Gwamnan jihar Yobe; Ibrahim Geidam

Da yake jawabi a yayin ci gaba da bincike akan zargin laifin zamba da ake yiwa shugaban NEMA, Mustapha Maihaja, Mista Lamin ya bayyana cewa jihar Yobe ta samu amfanin kayan agaji ne kadai daga kungiyoyi masu zaman kansu.

KARANTA KUMA: Jami'an 'Yan Sanda da Dakarun Soji sun mamaye majalisar Dokoki ta kasa

A na shi bangaren shugaban na NEMA ya bayyana cewa, ko shakka ba bu an rarraba kayan agaji a jihar amma ba zai iya tantance waɗanda suka yi ruwa da tsaki wajen wannan aiki ba, kazalika ba ya da wata rubutacciyar shaida da za ta tabbatar da hakan.

Mukaddashin kwamitin 'yan majalisar, Ali Isa dan jam'iyyar PDP na jihar Gombe, ya bayar da umarnin ga Mahaija akan gabatar da takardu gami da shaidu da za su tabbatar da hujjar sa a yayin zaman ta na ranar Talatar mako mai gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel