Sai an yi ruwan sama mu ke shan ruwa – inji ‘Yar Chibok da ta kubuta

Sai an yi ruwan sama mu ke shan ruwa – inji ‘Yar Chibok da ta kubuta

- Lydia Joshua tana cikin 'Yan matan da aka sace a Garin Chibok a 2014

- An sako ta a bara inda yanzu haka ta shiga Jami’ar Amurka da ke Yola

- Dangin Baiwar Allah sun bayyana irin mugun wahalar da ta sha a baya

Kwanan nan wata daga cikin ‘Yan matan Makarantar Chibok da Boko Haram su ka sace kwanaki ta bayyana irin wahalar da su ka sha a hannun ‘Yan ta’addan lokaci su na tsare a cikin Daji.

Sai an yi ruwan sama mu ke shan ruwa – inji ‘Yar Chibok da ta kubuta

'Yan Boko Haram sun sace mata 276 a Chibok a 2014

Lydia Joshua wanda tana cikin wadanda ‘Yan Boko Haram su ka sace a 2014 ta samu kubuta a 2017 bayan da Gwamnati ta sa baki aka saki wasu daga cikin su. Baiwar Allah tace ya kai ba su samun ko ruwan sha sai an yi ruwan sama.

KU KARANTA: Rahma Hassan ta samu haihuwar tsaleliyar yarinya

Wata daga cikin ‘Yan uwan yarinyar ta bayyanawa The Cable cewa ‘Yan ta’addan sun wahalar da ‘Yan matan musamman wadanda su ka ki auran su. Da zarar mace tace ba za ta auri ‘Yan ta’addan ba sai ayi ta guma mata azaba da wahala.

Joshua tace sun yi ta fama da macizai a inda su ke barci sannan kuma ga mahaukaciyar yunwa. Allah dai ya tsaga da rabon cewa Lydia za ta baro hannun Boko Haram wanda yanzu haka an sa ta a Jami’a domin cigaba da karatun Boko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel