An hallaka wasu ‘Yan ta'addan Boko Haram a Garin Gamborin Ngala

An hallaka wasu ‘Yan ta'addan Boko Haram a Garin Gamborin Ngala

- Sojoji sun damke wani da ake zargi babban ‘Dan Boko Haram ne

- An kuma yi nasarar hana wani bam da aka dasa a hanya tashi jiya

- Rundunar Operation lafiya dole sun kuma kashe wani ‘Dan ta’adda

Rundunar Sojin kasar nan sun tare da wani ‘Dan ta’addan Boko Haram mai suna Madaki Tumba a jiya Alhamis da makamai a Garin Gamboru Ngala lokacin da yake kokarin barin Dajin Sambisa kamar yadda mu ka samu labari dazu.

An hallaka wasu ‘Yan ta'addan Boko Haram a Garin Gamborin Ngala

Sojoji sun yi ram da Boko Haram a Sambisa inji Onyema Nwachukwu

Sojojin kasar sun kuma hallaka wasu ‘Yan ta’addan da dama a wata karawa da aka yi a jiya da yamma. Sojojin Najeriyar sun tare ‘Yan Boko Haram dinnen lokacin da su ke rike da bindigogi da kayan yaki a hanyar Garin Ngala.

KU KARANTA: An kama wani hatsabibin tsagera a Jihar Taraba

An dai dace a lokacin Jami’an tsaron kasar su na da manyan alburushi inda su ka shiga buda masu wuta. An samu karbe bindigar AK-47 da kuma harasashi daga hannun ‘Yan ta’addan. Da dama dai sun jikkata a harin na jiya.

Bayana nan kuma wasu Sojojin kasar na Operation lafiya doleda ke sintiri a hanyar Jebra zuwa Firgi sun yi nasarar hana wani bam da aka dasa da rana tashi. ‘Yan ta’addan sun sa bam dinne a wajen hanyar dajin Sambisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel