An gano sunan dalibar da suka yi waya da Farfesa mai rabon maki bayan lalata

An gano sunan dalibar da suka yi waya da Farfesa mai rabon maki bayan lalata

- Jami'ar Obafemi Awolowo da ke ile-ife ta bayyana wata daliba mai suna Monica Osagie a matsayin wadda tayi waya da Farfesa don samun maki bayan sunyi lalata

- Osagie dai tana karatun digirinta na biyu ne (Msc) a fannin kasuwanci wato Business Administration

- Shugaban jami'an yace ana kokarin tabbatar da hakan kafin hukumar binciken taji daga bakinta

Mahukuntan jami'ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife sun bayyana a ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu cewa wata dalibar makarantar mai suna Monica Osagie a matsayin wadda tayi waya da wani Farfesa don samun makin cin jarabawar data fadi a baya.

An gano sunan dalibar da suka yi waya da Farfesa mai rabon maki bayan lalata

An gano sunan dalibar da suka yi waya da Farfesa mai rabon maki bayan lalata

Shugaban Jami'an Farfesa, Eyitofe Ogunbodede yace Monica Osagie tana yin karatun digiri na biyu (Msc) dinta a bangaren Business Administration wato nazarin kasuwanci a makarantar.

DUBA WANNAN: Babu rashawa a fadar shugaban kasa - Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Ya bayyana cewa ana Tuhumar Farfesa Richard Akindele da nuna sha'awar sa akan hakan. Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta samu fefen murya da yake dauke da wata tattaunawa akan neman yarjewa wajen jima'i domin samun maki.

Shugaban jami'an yace hukumar ta nemi Osagie da Akindele dasu bayyana a gaban ta amma Akindele kadai yaje. Hukumar Jami'ar tana ci gaba da kokarin ganin Osagie ta je wajen hukumar domin taji daga bakinta ta samu damar hada dukkan wasu bayanai da za'a bukata.

Ya bayyana cewa dalilin dayasa har yanzu ba'a sallami Akindele daga aiki ba shine dole sai anbi duk wasu dokokin makarantar. Shugaban ya bayyana hakan a ranar Lahadi 15 ga watan Afrilu a yayin tattaunawa da manema labarai.

Yace har yanzu hukumar makarantar bata mika case din hannun hukumar yan sanda ba. Amma zasu nemesu idan wani Abu ya taso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel