Babu rashawa a fadar shugaban kasa - Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Babu rashawa a fadar shugaban kasa - Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa babu rashawa a cikin wannan jagoran cin.

- Yace matakin da gwamnatin ta dauka ya sanya tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa kamar yadda aka gani a harajin hukumomi kamar JAMB, FAAN, NPA da sauransu

- Osinbanjo kuma ya koka kan yadda gwamnatin data shude ta kashe kudaden kasa don yakin neman zabe

Farfesa Yemi Osinbajo (SAN) mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa a cikin wannan jagoran cin na shugaba Muhammad Buhari babu cin hanci da rashawa kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakane a yayin da Kungiyar 'yan kasuwa takai masa ziyara a ofishinsa dake Abuja. Kungiyar ra yan kwararun yan kasuwa musulmi sunce gwamnatin tayi tattalin kudade tun bayan hawanta kan mulki.

Babu rashawa a fadar shugaban kasa - Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Babu rashawa a fadar shugaban kasa - Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

DUBA WANNAN: Sarkin Daura ya roki shugaba Buhari ya sake duba batun Peace Corp

Ya kara da cewa "wani abu guda daya da muke da tabbacinsa a yanzu shine rashin cin hanci da rashawa, sannan shi kansa jagoran namu baya sata kuma bazai taba yiba. Hakan ya janyo kasar mu ta Tara kudade masu yawa a yanzu. Kamar abinda ya faru da JAMB, FIRS, NPA, FAAN, NIMASA wanda muka shaida ci gaba da aka samu."

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa wannan gwamnati ta samu nasarori da dama wanda ba'a samu ba kafin hawanta.

A furucin sa yace"ba wata gwamnati data samu nasarar da gwamnatin me ci yanzu ta samu, gwamnatocin baya sun ajjiye hakan a gefe yayin da suka ta'allaka a ranto kudade wanda suke salwantar dasu ta hanyar zabe."

Yana zargin gwamnatin data gabata ta Good luck Jonathan akan milliyoyin kudi wadanda akayi amfani dasu sati biyu kafin zaben 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel