Yadda akayi muka gano sandar iko na majalisa – Yan sanda

Yadda akayi muka gano sandar iko na majalisa – Yan sanda

- Hukumar ‘Yan Sanda ta gano Sandar Girma ta majalissa wadda wasu ‘yan ta’adda suka sace a ranar Laraba

- Mataimakin shugaban ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a SP Aremu Adeniran, yace sun gano Sandar ne karkashin gada ta City gate a birnin tarayyar an yadda ita

- Adeniran yace sun gano Sandar ne bayan umurnin da shugaban hukumar ‘Yan Sandan na kasa Ibrahim Idris ya bayar daga majalissar cewa a gano Sandar ta kowane hali

Hukumar ‘Yan Sanda ta gano Sandar Girma ta majalissa wadda wasu ‘yan ta’adda suka sace a ranar Laraba, daga majalissar zartarwa.

Mataimakin shugaban ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a SP Aremu Adeniran, yace sun gano Sandar ne karkashin gada ta City gate a birnin tarayyar an yadda ita, amma dai basu kama kowa ba har yanzu cikin wadanda ake zargin.

Yadda akayi muka gano sandar iko na majalisa – Yan sanda

Yadda akayi muka gano sandar iko na majalisa – Yan sanda

Adeniran yace sun gano Sandar ne bayan umurnin da shugaban hukumar ‘Yan Sandan na kasa Ibrahim Idris ya bayar daga majalissar cewa a gano Sandar ta kowane hali, inda ya bukaci a rufe kowace hanya dake birnin tarayyar har sai an gano masa Sandar.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bayar da belin yan Shia 22 da aka tsare

Yace wani cikin masu wucewa ne ya ganta karkashin gadar an yada ita ya sanar da hukumar ta ‘Yan Sanda, ya kara da cewa a nan ana cigaba da bincike har sai an gano wadanda suka aikata wannan laifi an hukuntasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel