2019: Bazamu iya kada APC ba idan bamu hada kawunan mu ba - PDP

2019: Bazamu iya kada APC ba idan bamu hada kawunan mu ba - PDP

- Ciyaman na tarayya na jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus yace jam’iyyar tasu bazata iya kada jam’iyyar adawa ta APC ba idan har basu hada kawunansu ba

- Secondus ya bayyana hakan ne a taron masu zartarwa na jam’iyyar ta PDP, inda yace sai sun hada kawunansu sannan zasu iya cire jam’iyyar adawa ta APC daga kan mulki

- Ciyaman na PDP ya danganta mulkin wannan gwamnatin da shigen mulkin Soja amma a fara hula da akayi a shekarar 1999

Ciyaman na tarayya na jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus yace jam’iyyar tasu bazata iya kada jam’iyyar adawa ta APC ba idan har basu hada kawunansu ba.

Secondus ya bayyana hakan ne a taron masu zartarwa na jam’iyyar ta PDP, inda yace sai sun hada kawunansu sannan zasu iya cire jam’iyyar adawa ta APC daga kan mulkin kasar nan.

2019: Bazamu iya kada APC ba idan bamu hada kawunan mu ba - PDP

2019: Bazamu iya kada APC ba idan bamu hada kawunan mu ba - PDP

Ciyaman na PDP ya danganta mulkin wannan gwamnatin da shigen mulkin Soja amma a fara hula da akayi a shekarar 1999, saboda haka ya zama wajibi su tabbatr da cewa sun kawo sabon shugaban kasa a Najeriya don cigaban al’umma.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo ya bukaci matasa dasu shiryawa jagorancin siyasa

Ciyaman na kungiyar masu zartarwa a jam’iyyar ta PDP, Sanata Walid Jibrin, ya jinjinawa ‘yan kungiyar zartarwar na jam’iyyar bisa kokarin da sukayi na hada kan jam’iyyar. Ya kuma roki Ubangiji yasa suci zabe a jihar Ekiti, saboda zai kara masu kwarin gwaiwa a zaben 2019 mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel