Wani jami’in Dansanda ya rasa ransa a yayin wani hari da yan bindiga suka kai Ofishin Yansanda

Wani jami’in Dansanda ya rasa ransa a yayin wani hari da yan bindiga suka kai Ofishin Yansanda

Wani jami’in Dansanda mai suna Abubakar Jibril ya rasa ransa a yayin da yan wasu yan bindiga suka kai ma Ofishin Yansanda hari, dake kauyen Kutigi na cikin karamar hukumar Lavun, na jihar Kebbi.

The Cable ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Muhammadu Abubakar ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 19 ga watan Afrilu, a shelkwatar rundunar Yansandan jihar.

KU KARANTA: Kuma dai: Yan bindiga suna fantsama jihar Filato sun bindige mutum 4 har lahira

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin na cewa yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 3:50 na daren Alhamis, inda suka kaddamar da harin mai kan uwa da wabi, sai dai Yansandan sun mayar da biki, amma jami’I guda ya rasu.

Wani jami’in Dansanda ya rasa ransa a yayin wani hari da yan bindiga suka kai Ofishin Yansanda

Ofishin Yansanda

Kaakakin ya cigaba da cewa kwamishinan Yansandan jihar ya kafa kwamitin bincike mai mambobi bakwai, a karkashin jagorancin babban jami’in Dansanda Abdullahi Tahir don bincikan musabbabin harin, tare da kamo masu laifin.

Daga karshe kwamishinan ya bayyana sun sanya kyautar naira dubu dari biyar, N500,000 ga duk wanda ya kawo muhimman bayanai da zai kai ga kama wadanda suka kai harin, sa’annan ya shawarci jama’a dasu taimaka ma rundunar wajen kama bata gari a jihar Neja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel