Rikicin jihar Taraba: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a Taraba

Rikicin jihar Taraba: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a Taraba

A ranar Alhamis, rundunar Sojojin Najeriya ta 101 ta cafke wani kasurgumin Dan bindiga a kauyen Zamban, cikin karamar hukumar Suntai na jihar Taraba, inda suka kwato makamai, inji rahoton Daily Trust.

Kaakakin rundunar Sojin, Birgedya Texas Chukwu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 19 ga watan Afrilu, inda yace Sojoji sun samu nasarar fatattakar wasu yan bindiga da suka kai hari wani kauye, wadanda ake zargin makiyaya ne yan Fulani.

KU KARANTA: Sabo da yi: Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sallamar Malamai 4,562 kan rashin iya rubuta wasika

Rikicin jihar Taraba: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a Taraba

Dan bindiga

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa a yayin rakiyar kuran da suka yi ma yan bindigar, sun samu nasarar kama guda daga cikinsu, inda a yanzu haka suna bincikensa.

Sai dai Kaakaki Texas Chukwu ya bayyana cewa sun kwato samfurin bindigu guda hudu, alburusai da dama, adduna 3, wayar salulu da sauran kayayyaki.

Rikicin jihar Taraba: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a Taraba

Dan bindigar

Daga karshe Texas ya bukaci jama’a dasu kai rahoton duk wani mutumin da basu gane take takensa ba a unguwanninsu ga hukumomin tsaro don daukar matakin daya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel