Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta fara gangamin yakin neman zabe a Legas

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta fara gangamin yakin neman zabe a Legas

Wata kungiya ta 'yan Najeriya masu ra'ayin dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 mai suna Re-building Nigeria Initiativeta a turance ayyana cewa ta shirya tsaf domin kaddamar da gangamin yakin neman zaben gwanin su a jihar Legas ranar Lahadi mai zuwa 22 ga watan Afrilu.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa baki daya Earnest Fasan shine ya kwarmatawa manema labarai hakan a garin na Legas inda kuma ya ce hakan na a matsayin wata 'yar manuniya ce ga wasu tarukan daban domin samun nasarar gwanin na su.

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta fara gangamin yakin neman zabe a Legas

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta fara gangamin yakin neman zabe a Legas

KU KARANTA: Malaman addinai a Arewa sun juyawa Buhari baya

A wani labarin kuma, Wata babbar kotun jiha da ke zaman ta a garin Kwale, karamar hukumar Ndokwa ta yamma ta tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Delta din mai suna Mista Friday Osanebi bisa zargin bayar da bayanan karya.

Kotun wadda Alkali V. I Ofezi ya shugabanta ta kuma umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau Independent Electoral Commission, INEC da ta gaggauta karbar shaidar zaben da ta bashi sannan ta mayar da shi ga Mista Emeka Odegbe wanda tace shine halastaccen dan takarar jam'iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel