An dakatar da wani na-kusa da Saraki daga Jam'iyyar APC a Kwara

An dakatar da wani na-kusa da Saraki daga Jam'iyyar APC a Kwara

- Jam'iyyar APC ta dakatar da wani tsohon 'Dan Majalisa kwanan nan

- Mashood Mustafa tsohon Hadimin Shugaban Majalisar Dattawa ne

- Honarabul Mustafa ya ki amsa goron gayyatar Jam’iyyar mai mulki

Dazu nan mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Jam'iyyar APC mai mulki a Jihar Kwara ta dakatar da wani tsohon 'Dan Majalisar dokokin Jihar watau Honarabul Mustafa Mashood.

Jam'iyyar mai mulki a Jihar Kwara da kuma Najeriya watau APC ta ce ta dakatar da Mustafa Mashood daga Jam'iyyar ne bayan ya sabawa gayyatar da tayi ta masa kwanakin baya. Don haka ya zama dole ya bar Jam'iyyar mai mulki.

KU KARANTA: Sanatan APC da aka dakatar yace bai da hannu a rikicin Majalisa ba

Shugaban Jam'iyyar a Yankin Alanamu a cikin karamar Hukumar Ilorin watau Abdurrahman Jimoh da Sakataren sa Abdulwasiu Kehinde su ka bayannan wannan a makon nan. Manyan Jam'iyyar sun yi na'am da wannan mataki.

Kwanan nan ne kuma Saraki ya sallami tsohon 'Dan Majalisar daga cikin masu ba shi shawara a kan harkokin musamman ya nada wani dabam. Har yanzu dai Honarabul Mustafa Mashood bai ce komai ba game da wannan batu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel