PDP zata yi maja: Muna tattaunawa da jam’iyyun adawa domin tunkarar 2019 – Secondus

PDP zata yi maja: Muna tattaunawa da jam’iyyun adawa domin tunkarar 2019 – Secondus

Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ya bayyana cewar suna tuntubar ragowar jam’iyyun adawa dake kasar nan da kungiyoyi da kuma tsofin shugabanni domin hada karfi da karfe a tunkari zaben shekarar 2019.

Da yake Magana a wurin taron jam’iyyar PDP na gaggawa, karo na 79, da ake yi a Abuja, secondus y ace zasu cigaba da tuntuba domin kafa wata tafiya mai karfi da zata samar dad an takara da zai lashe zaben shugabancin kasa ya ceto Najeriya daga mulkin kama karya.

Duk da bai yi Karin haske dangane da me suke shirya wa ko matsayar da suka cimma da ragowar jam’iyyun adawa ba, Secondus, y ace zasu bawa jam’iyyar APC kunya kamar yadda ta kunyata ‘yan Najeriya.

PDP zata yi maja: Muna tattaunawa da jam’iyyun adawa domin tunkarar 2019 – Secondus

Uche Secondus
Source: Depositphotos

Mun tuntubi jam’iyyun Najeriya da yawa. Kwanan nan zamu samar da wani dangi irin na siyasa mai karfin gaske a kasar nan da zai kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC. Muna kara kira ga ‘yan uwan mu maza da mata, manya da matasa da su zo mu hada karfi da karfe domin ceto kasar mu Najeriya daga kangin matsalolin fatara, talauci, durkushewar tattalin arziki, lalacewar siyasa da harkar tsaro,” a cewar Secondus.

DUBA WANNAN: Kanu ya bayyana dalilin ziyarar sa ga Sheikh Pantami, kalli hotunan ganawar su

Manyan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka halarci taron sun hada da gwamonin jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom, Ekiti; Ayo Fayose, Gombe; Ibrahim Hassan Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Jigawa; Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Neja; Babangida Aliyu, Tsohon gwamnan jihar Kaduna; Ramalan Yero da Ahmed Makarfi da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel