Limami ya tafka caca da kudin coci har dalar $620,000

Limami ya tafka caca da kudin coci har dalar $620,000

- Wani limamin coci, Falvio Gobbo, a ya bannatar da kudin coci har dalar Amurka 620,000 a wajen caca

- Gobbo ya yi hanzarin amsa laifinsa inda ya roki ayi masa sassauci cikin hunkunci

- An yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan yari tare da cewa zai tafi asibiti don ayi masa maganin cacar

Limami ya tafka caca da kudin coci har dalar $620,000

Limami ya tafka caca da kudin coci har dalar $620,000

Wani limamin coci, Flavio Gobbo a kasar Italiya ya kashe tsabar kudi dalar Amurka 620,000 mallakar cocin ta hanyar caca kamar yadda kafar yadda labarai na The Cable ta ruwaito.

Gobbo, mai shekaru 48 a duniya ya amsa laifinsa kuma ya roki alfarma inda aka rage masa hukuncin zuwa zaman gidan yari na shekaru biyu saboda laifin almubazaranci kamar yadda jaridar Corriere della Serra na kasar Italiya ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Hukumar sojin Najeriya tayi gargadi na musamman ga 'yan siyasa

A cikin hukuncin da ake yanke masa, yayi alkawarin cewa zai dawo da kudin a hankali kuma zai fara zuwa asibiti saboda ayi masa magani saboda ya dena yin cacan, sauran limaman cocin sunyi alakawarin taimaka masa.

"A wannan tafiyar mai tsawo da matukar wahala, Fada Flavio zayi dogaro da addu'o'i kuma muna fatan zai dawo ya cigaba da ayyukansa cikin kankanin lokaci," Inji cocin na Treviso a sanarwar da suka fitar.

Gobbo ya baro aikinsa a matsayin lamamin coci a Spinea, kusa da Venice a watan Octoban 2016. A wannan lokacin mahukuntan cocin sunce yana fama da matsanancin gajiya ne.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel