Hukumar Kwastam ta datse kayan Fasakauri na kimanin N65m a jihar Kaduna

Hukumar Kwastam ta datse kayan Fasakauri na kimanin N65m a jihar Kaduna

Hukumar Kastam ta hana fasakauri ta bayyana a ranar Alhamis cewa, cikin sauke nauyin da rataya a wuyanta ta yi nasarar datse haramtattun buhunan shinkafa 1, 500 da kuma man gyada na kimanin Naira miliyan 65 a jihar Kaduna.

Shugaban wannan reshe, Kwanturola Usman Dakingari shine ya bayyana hakan a yayin gabatarwa manema labarai kayan fasakaurin da suka dakile cikin wasu tireloli biyu da aka yi basaja da su ta danyar gyada da kuma citta.

Hukumar Kwastam ta datse kayan Fasakauri na kimanin N65m a jihar Kaduna

Hukumar Kwastam ta datse kayan Fasakauri na kimanin N65m a jihar Kaduna

Shugaban ya bayyana cewa, wannan manyan motoci sun yi lodi da ya ƙunshi buhunan shinkafa 1,500 wanda ke da nauyin haraji na kimanin N60m da kuma man gyada na kimanin N5m.

Dankingari ya ci gaba da cewa, hukumar ta yi wannan nasara ne a sanadiyar rahotanni daga wasu al'umma masu kishin kasar su ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Wasu Fursunoni 2 na Kirikiri sun fara karatun Digiri na Uku

Ya kara da cewa, hukumar ba za ta lamunci duk wani nau'i na fasakauri a reshen ba kuma a shirye ta wajen daukar mataki kan masu yiwa tattalin arziki zagon kasa.

A yayin haka kuma kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar ta yi nasarar datse wasu miyagun kwayoyi da suka hadar da Tramadol da Vi*gra a babbar hanyar Abuja zuwa Lokaja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel