Jami'an 'Yan Sanda da Dakarun Soji sun mamaye majalisar Dokoki ta kasa

Jami'an 'Yan Sanda da Dakarun Soji sun mamaye majalisar Dokoki ta kasa

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, an tsananta tsaro a yayin gudanar da zaman majalisar dokoki ta kasa na ranar Alhamis a sakamakon harin da 'yan tayar da zaune tsaye suka yi a ranar Larabar da ta gabata.

Batutuwan wannan hari sun gudana a harsunan dumbin al'umma a kasar nan da ma na kasashen ketare, yayin da tsagerun suka arce da sandar majalisar, wanda aka yi nasarar tsinto karkashin wata gada a safiyar yau a garin Abuja.

Jami'an 'Yan Sanda da Dakarun Soji sun mamaye majalisar Dokoki ta kasa

Jami'an 'Yan Sanda da Dakarun Soji sun mamaye majalisar Dokoki ta kasa

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya sanya jami'an hukumar 'yan sanda da dakarun soji suka mamaye duk wata haraba da farfajiyar majalisar domin tsananta tsaro gami da bincikar masu baki masu shige ta fice.

KARANTA KUMA: Jerin Mawaka 5 da suka fi kowa kudi a duniya

Sai dai wasu daga cikin dakarun sojin da jami'an 'yan sanda sun jayayya da juna dangane da hukumar da nauyin kare majalisar ya rataya a wuyanta., inda babban jami'in dan sanda mai kula da reshen majalisar, Mista A. Sulu- Gambari ya sulhunta lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel