Yanzu Yanzu: Fusatattun sojoji sun kai ramuwar gayya inda suka cinnama wani kauye wuta a jihar Benue

Yanzu Yanzu: Fusatattun sojoji sun kai ramuwar gayya inda suka cinnama wani kauye wuta a jihar Benue

Rahotanni sun kawo cewa wasu fusatattun sojin Najeriya sun kai farmaki wani gari a jihar Benue sannan sun cinna ma gidaje wuta, wani jami’i ya fadama jaridar Premium Times.

Sojojin sun kai hari Naka, mazaunin karamar hukumar Gwer West da misalin karfe 11:00 na safe sannan suka fara gona gidaje inda suka tsorata mazauna yankin, Francis Ayagah, shugaban karamar hukumar ya fadawa manema labarai ta wayan tarho a ranar Alhamis.

Yanzu Yanzu: Fusatattun sojoji sun kai ramuwar gayya inda suka cinnama wani kauye wuta a jihar Benue

Yanzu Yanzu: Fusatattun sojoji sun kai ramuwar gayya inda suka cinnama wani kauye wuta a jihar Benue

Babu wani cikakken bayani game da lamarin a bayyane sannan kuma a take Ayagah ba zai iya tabbatar da adadin mutane da abun ya shafa ba, idan akwai kenan.

KU KARANTA KUMA: APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

Amma dai yace sojojin sun kai ramuwar gayya ne na harin da akai inda aka kashe wani abokin aikinsu a garin a ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel