Dakyau: Wasu tsageru 20 da shugaban kungiyar su dake tayar da hankula a Zamfara sun shiga hannu

Dakyau: Wasu tsageru 20 da shugaban kungiyar su dake tayar da hankula a Zamfara sun shiga hannu

Shugaban wata kungiyar tsageru da yaran sa 20 dake haddasa rigingimu a garin Gusay dake jihar Zamfara sun shiga hannu.

Hukumar 'yan sanda a jihar Zamfara ta ce ta kama kasurgumin dan ta'adda dake jagorantar wasu 'yan sara-suka a jihar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau ta bakin kakakinta, DSP Muhammad Shehu, ta ce ta kama shugaban kungiyar da yaran sa 20 da suka dade suna tayar da hankulan mazauna Gusau, babban birnin jihar.

Dakyau: Wasu tsageru 20 da shugaban kungiyar su dake tayar da hankula a Zamfara sun shiga hannu

Gwamnan Jihar Zamfara; Andulaziz Yari

Sanarwar ta ce an kama 'yan ta'addar da shugaban nasu ne a jiya, Laraba, a unguwar 'Yan-Magwarora, yayin wani samame da hukumar ta kai a mafakar bata gari daban-daban a fadin garin Gusau.

Hukumar ta ce ta samu tabar wiwi da wasu kwayoyin maye a sansanin 'yan ta'addar.

DUBA WANNAN: Kwamishina da ma'aikatan Bauchi 54 sun shiga tsaka mai wuya, kotun da'ar ma'aikata zata koma jihar saboda su

Sanarwar ta bayyana cewar wadanda aka kama din na taimakawa jami'an 'yan sanda da muhimman bayanai tare da bayyana cewar, hukumar na cigaba da farautar 'yan kungiyar.

Hukumar 'yan sandan ta ce ba zata taba gajiyawa ba a yakin da take yi da 'yan ta'adda da bata gari ba tare da jaddada aniyar ta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel