Majalisa na nan akan bakanta game da dakatar da Munir Gwarzo daga matsayinsa na Darakta Janar

Majalisa na nan akan bakanta game da dakatar da Munir Gwarzo daga matsayinsa na Darakta Janar

- Majalisar wakilai ta bayyana cewa tana nan akan bakanta kan maganar dakatar da Mounir Gwarzo daga matsayin Darakta Janar na hukumar tsaro da canji

- Majalisar lokacin da aka gabatar mata da rahoto daga kwamitin majalissar na kasuwanci da jami’u wanda Tajuddeen Ayo Yusuf ke jagoranta

- Tajuddeen yace tabbas Gwarzo ya aikata laifi kuma Ministan kudi Kemi Adeosun yayi daidai da ya dakatar da Gwarzo

Majalisar wakilai ta bayyana cewa tana nan akan bakanta kan maganar dakatar da Mounir Gwarzo daga matsayin Darakta Janar na hukumar tsaro da canji (SEC).

Majalisar lokacin da aka gabatar mata da rahoto a ranar daga kwamitin majalissar na kasuwanci da jami’u wanda Tajuddeen Ayo Yususf (PDP, Kogi) yake jagoranta yace tabbas Gwarzo ya aikata laifi kuma Ministan kudi Kemi Adeosun yayi daidai da ya dakatar da Gwarzo.

Majalisa na nan akan bakanta game da dakatar da Munir Gwarzo daga matsayinsa na Darakta Janar

Majalisa na nan akan bakanta game da dakatar da Munir Gwarzo daga matsayinsa na Darakta Janar

Dangane da korafe korafe da masu ruwa da tsaki daban daban suka kawo, ya sanya dole majalissar tayi bincike a kan kamfanin Oando plc. Bayan haka majalissar ace mai’aikatan hukumar ta SEC biyu da suma aka dakatar Mrs Anastacia Braimoh da Naif Abdulsalam su dawo bakin aikinsu cikin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

Yusuf wanda shine ciyaman na kwamitin, lokacin da yakewa abokan aikinsa jawabi akan binciken da sukayi, yace Gwarzo ya kasance Darakta a wani kamfani mai zaman kansa duk da cewa yana shugaban hukumar ta SEC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel