Babu inda za ka, kotu tayi fatali da bukatar tsohon sakataren yada labaran PDP

Babu inda za ka, kotu tayi fatali da bukatar tsohon sakataren yada labaran PDP

- Kotu tayi watsi da bukatar tsohon kakakin jam'iyyar PDP, Olisah Metuh, na fita kasar wajen don ganin likita

- Kotun tace wannan shine karo na uku da Metuh yake shigar da irin wannan bukatar a maimakon ya kare kansa kawai

- Kotun tace tana zargin akwai wata makarkashiya dayake shiryawa, kuma ta dage cigaba da sauraron karar zuwa 20 ga watan Afrilu

A yau Alhamis ne Kotu tayi watsi da bukatar tsohon skataren yada labarai na jam'iyyar PDP, Olisah Metuh, na neman izinin tafiyar kasar waje don ganin likitocinsa duk da cewa ya gabatar da takardan shedan rashin lafiya daga wata asibiti a kasar Ingila.

Mr. Metuh yana fuskantar tuhume-tuhume wanda suka hada da karkatar da kudi miliyan N400 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a fanin tsaro, Kwanel Sambo Dasuki (murabus) duk da cewa an kawo shi kotu a gadon daukan marasa lafiya.

Babu inda za ka, kotu tayi fatali da bukatar tsohon sakataren yada labaran PDP

Babu inda za ka, kotu tayi fatali da bukatar tsohon sakataren yada labaran PDP

DUBA WANNAN: Za a gurfanar da tsohon gwamna Shema a kotu bisa badakalar kudin SURE-P naira 5.7bn

Lauya mai kula da shari'ar, Okong Abang ya dage sauraron bukatar tafiyar na Metuh har zuwa ranar Alhamis mai zuwa, Alkalin ya kuma tunatar da cewa a baya wata kotun tayi watsi da wata bukatar mai kama da wannan da Metuh ya gabatar.

Alkalin kotun ya nuna rashin gamsuwar sa kan yadda Mr. Metuh ya saka gabatar da wannan bukatar inda ya kara da cewa kotunsa bata da ikon canja hukuncin da kotun da farko ta yanke.

A cewar lauyoyin tsohon mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP, Mr. Metuh yana fama da ciwon kashin baya ne kuma yana bukatar likitoci su duba shi cikin gaggawa. Lauyoyin Metuh sun bukaci kotu ta basu lokaci mai tsawo saboda wanda suke karewa a samu sauki hakan yasa ma aka kawo shi kotu a gadon daukan marasa lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel