APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

- Sakataren tarayya na jam’iyyar APC na tarayya Timi Frank, ya bukaci shugaba Buhari da ya bawa matasan Niajeriya hakuri game da maganar da yayi cewa suna da son banza

- Buhari yace sama da 60% na matsan Najeriya basu wuce shekara 30 da haihuwa ba, kuma dayawa cikinsu basa zuwa makarata suna cewa Najeriya tana da arzikin man fetur

- Saboda haka sai suyi kwance a gida basu aikin komai amma suna son su samu kudi, suyi gidaje, su kuma samu ilimi kyauta kuma a kula da lafiyarsu kyauta

Sakataren tarayya na jam’iyyar APC na tarayya Timi Frank, ya bukaci shugaba Buhari da ya bawa matasan Niajeriya hakuri game da maganar da yayi cewa suna da son banza.

Dailytrust ta ruwaito cewa shugaba Buhari ya bayyana cewa sama da 60% na matasan Najeriya basu wuce shekara 30 da haihuwa ba, kuma dayawa cikinsu basa zuwa makarata suna cewa Najeriya tana da arzikin man fetur, a lokacin da yake jawabi ga kungiyar Westminsta a ranar Laraba kasar Ingila.

APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

Saboda haka sai suyi kwance a gida basu aikin komai amma suna son su samu kudi, suyi gidaje, su kuma samu ilimi kyauta kuma a kula da lafiyarsu kyauta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An mayar da sandar iko da aka sace majalisa

Sakamakon haka Sakatren jam’iyyar ta APC yace laifin shugaba Buhari ne saboda shine bai basu dama ba, saboda haka bai kamata ya zubar musu da kima ba a idon duniya, musamman a wurin taro na ‘yan kasuwar duniya.

Mista Frank a jawabin da yayi a ranar Alhamis, yana tinawa shugaba Buhari cewa sama da matasa 20 ne suka rasa rayukansu a shekara 2014 a kokarin neman aikin Jami’an gudun hijira na Najeriya.

Ya kara da cewa laifin shuwagabannin mu ne da basu kawo abubuwan cigaba wanda zai samarwa matan aiki shiyasa suke zaman banza.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel