Wani kwamishina da ma'aikatan jihar Bauchi 54 sun shiga tsaka mai wuya, kotun da'ar ma'aikata zata koma jihar Bauchi saboda su

Wani kwamishina da ma'aikatan jihar Bauchi 54 sun shiga tsaka mai wuya, kotun da'ar ma'aikata zata koma jihar Bauchi saboda su

Kotun da'ar ma'aikata (CCT) ta bayyana shirin ta na komawa jihar Bauchi domin fara shari'ar wani kwamishina da ma'aikatan 54 dake aiki a jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Ibraheem AL- Hassan ya sanar da hakan a jiya, Laraba.

AL-Hassan ya ce za a fara sauraron karar da hukumar CCT ta shigar da mutanen a babbar kotun jihar Bauchi daga ranar 24 zuwa 27 ga wata.

Ya bayyana cewar wadanda za a gurfanar din sun hada da masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi da kuma wasu mutane tara dake aiki karkashin ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Wani kwamishina da ma'aikatan jihar Bauchi 54 sun shiga tsaka mai wuya, kotun da'ar ma'aikata zata koma jihar Bauchi saboda su

Kotun da'ar ma'aikata

Ragowar sun hada da masu taimakawa gwamnan jihar mutum uku, ma'aikatan hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi NDLEA) mutum hudu da suka hada da kwamandan hukumar na jihar, 'yan sanda takwas da wani babban jami'in hukumar kwastam.

DUBA WANNAN: Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai

Ya kara da cewar, yayin gurfanar da mutanen, kotun da'ar ma'aikatan zata koma jihar kacokan.

AL-Hassan ya kara da cewar zasu yi amfani da damar da suke da ita wajen kara fadakar wa tare da wayar da kan ma'aikatan jihar dangane da aiyukan hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel