Yanzu Yanzu: An mayar da sandar iko da aka sace majalisa

Yanzu Yanzu: An mayar da sandar iko da aka sace majalisa

An dawo da sandar iko na majalisar dattawa da aka sace a ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu.

Wasu yan iska da ake zargin suna yiwa Sanata Ovie Omo-agege ne suka sace sandar daga zangon majalisa a ranar Laraban.

A martaninta majalisar dattawan ta ba hukumomin tsaro sa’’o’i 24 domin su nemo sandar wanda aka sace.

A safiyar ranar Alhamis ne hukumar yan sanda ta sanar da cewar anga sandar a karkashin wani gada a Abuja.

Yan sa’o’i kadan bayan wannan sanarwar, yan sanda sun dawo da sandar ga majalisar dokoki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: 'Yan sanda sun kamo 'yan ta'addan da suka sace sandar Majalisa (hotuna)

Da misalin karfe 11:50 na safe, wata mataimakiyar sufeto janar nay an sanda, Habila Joshak ta mika sandar ga magatakardan majalisar, Mohammed Sani-Omolori.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel