Da dumin sa: Dakarun soji sun dakile wani hari da aka kai masu, sun kama shugaban 'yan ta'addar

Da dumin sa: Dakarun soji sun dakile wani hari da aka kai masu, sun kama shugaban 'yan ta'addar

Hukumar sojin Najeriya ta ce dakarunta na runduna 101 dake atisayen AYEM AKPATUMA a jihar Taraba sun yi nasarar dakile wani hari da aka kai masu.

An kai wa dakarun sojojin harin ne yayin da suke sintiri a jiya Laraba a kauyen Zamban dake karamar hukumar Suntai.

Dakarun sojin sun bayyana cewar wasu makiyaya 'yan ta'adda ne suka kai masu hari amma sun dakile yunkurin su tare da kama wanda ake zargi shine jagoran makiyayan.

Da dumin sa: Dakarun soji sun dakile wani hari da aka kai masu, sun kama shugaban 'yan ta'addar

Dakarun soji

Hukumar sojin ta lissafa makamai da ta ce ta kwace daga hannun makiyayan, makaman sun hada da: bindiga samfurin AK-47 guda daya, wata babbar bindiga guda, bindigar baushe guda uku, wata bindiga ta musamman guda daya, alburusai, adduna, wukake da sauran su.

DUBA WANNAN: Yadda ake sace maza a yi masu auren dole a kasar Indiya

Ana cigaba da binciken wanda aka kama daga cikin wadanda suka kai harin.

Sanarwar, kamar yadda kakakin rundunar soji, Janar Texas Chukwu, ya fitar, ta bukaci jama'a da su sanar da hukumar duk wani motsin da basu yarda da shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel