Gwamnatin jihar Neja za ta dauki matasa 500 aiki domin rage zaman banza

Gwamnatin jihar Neja za ta dauki matasa 500 aiki domin rage zaman banza

Gwamnatin jihar Neja ta kudiri aniyyar yiwa wasu matasa 500 goma ta arziki dake aikin sa kai a hanyoyi yayin da take shirin daukar su aiki domin karfafa gwiwar su ta dakile zaman kashe wando da mutuwar zuciya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta ruwaito cewa, wannan matasa sun fara aikin sa kai ne bisa ga lamuni na tsohuwar gwamnatin jam'iyyar PDP ta jihar karkashin jagorancin gwamna Babangida Aliyu.

Gwamnatin jihar Neja za ta dauki matasa 500 aiki domin rage zaman banza

Gwamnatin jihar Neja za ta dauki matasa 500 aiki domin rage zaman banza

Kwamishinan sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Fanti, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar dake birnin Minna a ranar Alhamis.

KARANTA KUMA: Wani Mahaifi ya ƙone 'Dan sa da Dutsen guga mai zafi kuma ya antaya ma sa Fitsari

Fanti ya bayyana cewa, tuni gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai yi ruwa da tsaki wajen tantancewa tare da daukar matasan aiki.

A yayin haka kuma, kwamishinan kananan hukumomin na jihar Alhaji Zakari Jikantoro, ya bayar da shaida ta cewar gwamnatin ta kammala shirye-shiryen sayen motoci takwas kirar Toyota Prado akan kudi na N374.5m domin rabawa sarakunan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel