'Yan kasuwar Kano na neman shiga Takun Saka da Hukumar Kwastam

'Yan kasuwar Kano na neman shiga Takun Saka da Hukumar Kwastam

Wasu 'yan Kasuwar Kano sun bayyana damuwar su dangane da yadda jami'ai na hukumar Kwastam ke karbe masu abin hannu a yayin da suke safarar kayayyakin su na kasuwanci daga biranen Fatakwal, Legas da kuma Aba.

Wannan korafi yazo ne da sanadin shugaban kungiyar 'yan kasuwar jihar Kano masu sana'ar kayan kananan yara da na mata, Alhaji Dayyabu Salisu Sa'adu, inda yace daga garin Onitsha zuwa Kano akwai kimanin sansanai takwas na hukumar kwastam.

Alhaji Dayyabu ya bayyana cewa, a cikin kowane sansanai takwas din nan su kan biya kimanin Naira dubu biyar ga jami'an, inda akalla motoci 15 na 'yan kasuwar ke safara a hanya.

'Yan kasuwar Kano na neman shiga Takun Saka da Hukumar Kwastam

'Yan kasuwar Kano na neman shiga Takun Saka da Hukumar Kwastam

Baya ga haka shugaban kungiyar ya bayyana yadda wannan lamari yafi ci masu tuwo a kwarya a kan hanyar Legas, inda sansanai 14 na hukumar kwastam ke karbar N9,000 akan kowace motar su ta kaya.

Legit.ng ta fahimci cewa baya ga korafin 'yan kasuwar jihar Kano, takwarorin su na jihohin Neja, Kaduna, Filato da kuma Katsina sun koka da irin wannan cuzguni na jami'an hukumar kwastam.

KARANTA KUMA: Tsautsayi: 'Daliban Najeriya 3 sun riga mu gidan gaskiya a kasar Kamaru

A martanin da hukumar ta kwastam ta mayar, Mr. Joseph Attah, Kakakin hukumar kwastam mai shalkwata a birnin tarayya Abuja ya ce za su hukumta duk wani jami’insu da aka samu yana irin wannan dabi'ar.

A jawabin kakakin hukumar kwastam na kasa baki daya, Mista Joseph Attah, ya murza gashin baki gami da daga gashin gira kan jami'an su masu wannan bakin hali, inda ya ce duk wanda aka cafke cikin wannan harka ta bakin hali to ya kuka da kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel