Sabo da yi: Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sallamar Malamai 4,562 kan rashin iya rubuta wasika

Sabo da yi: Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sallamar Malamai 4,562 kan rashin iya rubuta wasika

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sallamar Malamai guda dubu arba’in da dari biyar da Sittin da biyu, 4562, daga cikin sabbin Malaman da ta dauka don su maye gurbin Malamai dubu ashirin da biyar da aka kora da basu cancanta ba.

Vanguard ta ruwaito gwamnati ta yanke shawarar sallamar sabbin Malaman ne bayan fadawa wata tarkon rago da ta shirya musu a yayin basu takardar kama aiki, inda ta umarce kowanne sabon Malami ya rubuta wasikar karbar aiki, amma da dama daga cikinsu suka gagara.

KU KARANTA: An kashe maciji ba’a sare kansa ba: Yaran Buharin Daji sun hallaka wasu mutane 2 a jihar Zamfara

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna, Jafaaru Sani ya bayyana haka a ranar Laraba 18 ga watan Afrilu, inda yace an sallami Malaman nan ne saboda ta tabbata basu cancanci samun aikin ba tun a farko.

Saba da yi: Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sallamar Malamai 4,562 kan rashin iya rubuta wasika

Malamai

Idan za’a tuna a kwanankin baya ne gwamnatin jihar Kaduna ta sallamai Malamai dubu ashirin da biyu, wadanda suka fadi jarabawar gwaji da ta shirya musu, jarabwar yan aji hudu, inda ta dauki sabbin Malamai dubu goma sha biyar, yayin da ake tsimayin daukan wasu dubu goma sababbi.

“Bayan mun kammala daukan sabbin Malaman aiki, sai muka umarci kowannensu ya rubuta wasikar karbar aiki, anan ne muka kama da dama daga cikinsu da rashn iya rubuta wasikar, don haka muka sake tantance Malaman gaba daya, inda muka gani 4,562 basu da inganci, yayin da 11,335 suka haye.

“A yanzu haa mun tura tatattun su 11,335 zuwa makarantun Firamari dubu husu da zasu koyar, da dama daga cikinsu na dauke da digiri ne, wasu kuma digiri na biyu, sai dai kafin nan sai da muka basu horo na musamman kan dabarun koyarwa, tare da sauran tsofaffin Malaman.” Inji shi.

Daga karshe Kwamishina Jaafaru ya bayyana cewa yana sa ran zasu kammala aikin daukan sabbin Malamai 13,665 daga yanzu zuwa sabuwar wata, don cika adadin Malaman da gwamnati ta yi alkawarin dauka, dubu ashirin da biyar, 25,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel