Atiku ya bayyana rashin amincewa da kalaman Buhari a kan matasan Najeriya

Atiku ya bayyana rashin amincewa da kalaman Buhari a kan matasan Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana akan a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis inda yake cewa bazai taba kwatanta cewa matasan Najeriya na zaman kashe wando ba. Yace matasan suna aiki tukuru wanda a karkashin sa akwai matasa sama da dubu da suke aiki dashi.

Shugaba Buhari ya furta hakane a Yayin wata tattaunawa dayayi ranar Laraba a Landan. Inda yake cewa "Da yawa daga cikinsu basa zuwa makaranta sannan suna cewa Najeriya tana da man fetur saboda haka zasu koma su zauna suna jiran a basu gida, kulawa da lafiya da kuma ilimi duk a kyauta"

Matasan Najeriya ba ragwaye bane: Martanin Atiku ga shugaba Buhari

Matasan Najeriya ba ragwaye bane: Martanin Atiku ga shugaba Buhari

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta roki ma'aikatan lafiya su janye yajin aikin da suka tafi

Atiku ya ce shi a gurinsa man fetur bashi kadai ne abin dogaro ba. Babban abin dogaran mu shine matasan mu da suke shirya fina finai. Yace matasan suna kokari wajen kirkirar abubuwa wanda zasu dogara da kansu.

Sannan tsohon mataimakin shugaban kasa Good luck Jonathan Reno Omekri a shafinsa na twitter yace matasan suna shirya fina finai ba tare da sa hannun gwamnati a ciki ba, sannan 77% na likitoci bakaken fata dake aiki a Amurka duk yan Nigeria ne. Shin Buhari zai iya bayyana wani abu guda daya da yayi nasara akansa?

A tsakanin matasan Najeriya da Buhari waye yake zaman banza? Wane shugaba ne zai zauna a gida yayi aiki wai bera na damunsa a Ofis. Zakaji daga garesu a 2019.

Wannan shine martani zuwa ga Buhari daya kira matasa masu zaman banza. Wannan yasa na kara girmama furfura ta tunda dai ni ba matashi bane kuma bamai zaman banza ba kamar yanda Buhari ya fada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel