Mai yayi zafi: PDP na tunanin canza sunanta kafin zaben 2019

Mai yayi zafi: PDP na tunanin canza sunanta kafin zaben 2019

- A yunƙurin PDP na cin zaɓen 2019, yanzu haka har ta kai ga tunanin sauya suna

- Taron na yau zau duba yiwuwar canzawa ko cigaba da amfani da sunan PDP

- Wannan dai ya biyo bayan zawarcin da PDP ke yiwa tsoffin mambobinta da suka sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun

Wasu rahotanni na nuni da cewa, yanzu haka dai jamiyyar PDP na shawarar canza sunanta kafin zaben 2019, a wani taron gaggawa da ta kira yau.

Hakan ya biyo bayan sharaɗin da waɗanda suka bar jam'iyyar a 2015 suka gindaya kafin dawowarsu cikinta.

An dai bayyana cewa, batun canza sunan na ɗaya daga cikin batutuwan da za'a tattauna a taron gaggawar da jam'iyyar ta kira kwamitin zartarwa da za'a gudanar yau Alhamis a Abuja.

A wani jawabi da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar na ƙasa ya fitar, Mr. Kola Ologbondiyan yace, taron kwamitin zai gudana ne a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa. Amma sai dai bai bayyana cewa ko za'a tattauna batun canjin sunan ba.

Mai yayi zafi: PDP na tunanin canza sunanta kafin zaben 2019

Kola Ologbondiyan

KU KARANTA: Wani rikakken Farfesa a Jami'ar ABU Zaria ya rasu kwatsam

Sai dai kuma an rawaito cewa, shugabancin jam'iyyar, zai yi amfani da wannan damar wajen shaidawa kwamitin zartarwa da sauran mambobin jam'iyyar shawara da sharaɗin da waɗanda suka fice daga jam'iyyar su kayi na cewa a canza sunan jam'iyyar gabannin zaɓen 2019 mutuƙar ana so su dawo. Kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

Wani jigo a jam'iyyar ta PDP da ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya tabbatarwa da majiyarmu cewa, tabbas yau za'a yanke hukunci kan batun canzawa ko kuma cigaba da amfani da sunan PDP

A cewarsa, "Gaskiya ne wasu da muka nemi su dawo sun gindaya sharadin sai mun canza suna, amma al'amari ne da ba za mu iya amsawa mu kaɗai ba, dole sai da sahalewar ragowar ƴan jam'iyya. Kuma dole ne muyi taka tsan-tsan don kar a yaudare mu, ayi mana in giza mai kantu cikin ruwa".

Sai dai kuma bayan tuntuɓar sakataren jam'iyyar na kasa Ologbondiyan kan batun, yace, shi bai da masaniyar abubuwan da za'a tattauna a wajen taron.

"Sai gobe za'a faɗi abinda za'a tattauna a wurin taron, ba abu ne da zan faɗa muku yanzu ba, don ban sani ba" ya fada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel