Wasu Fursunoni 2 na Kirikiri sun fara karatun Digiri na Uku

Wasu Fursunoni 2 na Kirikiri sun fara karatun Digiri na Uku

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Premium Times sun bayyana cewa, wasu fursunoni biyu dake gidan wakafi na Kirikiri a jihar Legas sun juya bayansu ga mutuwar zuciya yayin da suka fara karatun Digiri na uku a jami'ar NOUN.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wannan fursoni biyu suna cikin fursunoni uku da suka kammala karatun digiri na biyu a kwanakin baya.

Wasu Fursunoni 2 na Kirikiri sun fara karatun Digiri na Uku

Wasu Fursunoni 2 na Kirikiri sun fara karatun Digiri na Uku

Legit.ng ta fahimci cewa, sabuwar hanyar gudanar da karatu ta yanar gizo da jami'ar NOUN ke aiwatarwa a halin yanzu ita ta bayar da dama ga fursunonin su yi karatun su a saukake, inda adadin masu fursunonin na Kirikiri ya kai kimanin dari hudu.

KARANTA KUMA: Za mu iya rufe Majalisa domin tallafawa Buhari kawo karshen kashe-kashe - Ekweremadu

Tunwashe Kabiru da Oladipupo Moshood su ne fursunoni masu karatun digirgir, yayin da kwaturola Janar na hukumar gidajen yarin kasar nan, Ja’afaru Ahmed, ya nemi sauran fursunoni akan yin amfani da wannan dama da jami'ar NOUN ta bayar.

Shugaban jami'ar ta NOUN, Abdallah Adamu, ya yi kira ga fursunonin kasar wajen tanadin yanayi mai inganci tare da kayan karatu muhimman a gidajen wakafi da zasu saukakawa fursunoni a yayin nazari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel