Satar sanda: Sanatan APC yace babu sa hannun shi a rikicin Majalisa

Satar sanda: Sanatan APC yace babu sa hannun shi a rikicin Majalisa

Sanata Ovie Omo-Agege na Jam'iyyar APC wanda ake zargi da shigo da Tsageru cikin Majalisar Dattawa har su ka dauke sandar girma ana cikin zama yayi jawabi bayan Jami’an ‘Yan Sanda sun sake shi jiya inda ya wanke kan sa.

Sanata Omo-Agege ya wanke kan sa daga zargin cewa shi ya kawo ‘Yan daba cikin Majalisa a jiya Laraba. ‘Dan Majalisar yace ya tafi ofishin sa ne domin yayi aiki kamar yadda ya saba a kowace rana a jiya da abin ya auku.

Satar sanda: Sanatan APC yace babu sa hannun shi a rikicin Majalisa

Sanatan APC da aka dakatar yace bai san wadanda su ka tada hatsaniya a Majalisa ba

Omo-Agege wanda aka dakatar daga Majalisar Dattawa a makon jiya yace ya tuntubi masana shari’a kuma su ka ba shi shawarar ya koma bakin-aikin sa. A dalilin haka ne yace ya zo Majalisa ya zauna duk da an dakaytar da shi.

KU KARANTA: An sace wani Sanata a Majalisar Dattawan Najeriya jiya

‘Dan Majalisar yace akwai fin-karfi wajen dakatar da shi da aka yi don haka ne da ya shigo cikin Majalisa har wasu ‘Yan uwan sa su kayi murnar ganin sa. Sanatan ya karyata Majalisar da tace shi ya shigo da tsagerun ta bakin Aliyu Sabi.

Sanata Ovie Omo-Agege yace ya bar ‘Yan Sanda su yi bincike game da lamarin don kuwa aikin su ne yayin da shi kuma yake tunani kan kazafin da mai magana da bakin Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi yayi masa jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel