Hukumar 'Yan sanda tayi gum da bakinta game da 'yan Shi'a da aka sake kama wa

Hukumar 'Yan sanda tayi gum da bakinta game da 'yan Shi'a da aka sake kama wa

- Hukumar Yan sandan Najeriya taki bayar da bayyani akan adadin yan Shia da aka kama bayan kamun da akayi a ranar Litinin

- Yan Shi'a dai sun fara gudanar da tattaki ne a tittuna garin Abuja inda suke bukatar a saki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

- Mai magana da yawun yan Shi'an yayi ikirarin cewa yan sandan sun sake cika motocci uku makil da yan Shi'a a ranar Talata kuma suka tafi dasu

Har yanzu, Hukumar Yan sandan Najeriya taki cewa komai game da adadin yan Shi'a da aka kama tun bayan da ta tabbatar da cewa ta kama mutane 115 a ranar Litini da ta gabata a babban birnin tarayya Abuja.

'Yan Shi'an dai sun fara gudanar ta tattaki ne a titunan garin Abuja tun ranar Litinin inda suke bukatar gwamnati ta sako shugaban su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda aka kama bayan arangamar da 'yan kungiyar sukayi da sojojin Najeriya a Decembar 2015.

Hukumar 'Yan sanda tayi gum da bakinta game da 'yan Shi'a da ake sake kama wa

Hukumar 'Yan sanda tayi gum da bakinta game da 'yan Shi'a da ake sake kama wa

DUBA WANNAN: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da Sanata Ovie Omo-Agege

Wata babban kotu da ke Abuja ta bayar da umurnin sakin Sheikh El-Zakzaky a Decembar 2016 amma gwamnatin Najeriya ta daukaka kara kuma ta cigaba da tsare shugaban kungiyar tare da matarsa duk da cewa ba'a gurfanar dasu a bisa wani laifi ba tun bayan kama su.

A cewar mai magana da yawun yan Shi'a, Abdullahi Musa, "Yan sanda sun cika manyan motocci guda uku makil da yan shi'a da kuma wata karamar mota a ranar Laraba." Ya kuma kara da cewa hakan ba zai sa su dena gudanar da tattakin ba.

Duk da cewa yan sandan sunyi ta arangama da yan Shi'an a ranakun Talata da Laraba a Abuja, Kakakin hukumar Yan sanda baiyi tsokaci a kan batun ba lokacin da manema labarai daga jaridar Premium Times suka tuntube shi.

Bayan yayi ikirarin cewa bashi da masaniya akan abinda ya faru a ranar Talata, Kakakin hukumar Yan sandan, Manzah Anjuguri, yaki amsa wayarsa har zuwa ranar Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel