Sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na wadanda suka saci kudin gwamnati yarinta ne - Dickson

Sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na wadanda suka saci kudin gwamnati yarinta ne - Dickson

- Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa cin mutuncin jam’iyyar PDP ne wanda jam’iyyar APC keyi na fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati

- Dickson yace gwamnatin APC su mayar da hankali akan ayyukan da suka yiwa ’yan Najeriya ba wai su tsaya suna fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati ba

- Shugaban labarai na gwamnan Mr. Francis Ottah Agbo, yace gwamna Dickson ya bayyana hakane lokacin da yake ganawa da manema labarai

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa cin mutuncin jam’iyyar PDP ne wanda jam’iyyar APC keyi na fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati.

Dickson yace gwamnatin APC su mayar da hankali akan ayyukan da suka yiwa ’yan Najeriya ba wai su tsaya suna fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati ba, don ba shine suka yiwa ‘yan Najeriya alkawari ba.

Shugaban labarai na gwamnan Mr. Francis Ottah Agbo, yace gwamna Dickson ya bayyana hakane lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Laraba, a Ofishinsa dake Yenagoa.

Sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na wadanda suka saci kudin gwamnati yarinta ne - Dickson

Sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na wadanda suka saci kudin gwamnati yarinta ne - Dickson
Source: Depositphotos

Yace ya amince da cewa dole a samu jam’iyyar adawa a cikin kasa daya, wanda wannan shine abunda jam’iyyar ta APC ta kasa fahimta kenan wanda hakan ya rikicewar jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojin Najeriya sunyi nasarar dakile wani hari a jihar Taraba (hotuna)

Dickson yace ya kamata gwamnatin APC ya kamata su mayar da hankali wurin ganin sun magance matsalar rashin tsaro da kuma tattalin arzikin kasa ba wai su ringa yin abubuwan yarinta ba, da kokarin ciwa jami’iyyar PDP mutunci ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel