Babu wanda ya isa yayi mana barazana a Majalisa inji Bukola Saraki

Babu wanda ya isa yayi mana barazana a Majalisa inji Bukola Saraki

- Bukola Saraki yayi magana bayan an sungume sandar Majalisa

- Shugaban Majalisar yace babu wanda ya isa ya taka masu burki

- Saraki ya nemi a hukunta wadanda su kayi ta’adi a Majalisa jiya

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya aikowa ‘Yan Majalisar kasar nan sako bayan an sace sandar girma a jiya Laraba ana tsakiyar zama. A lokacin da abin ya faru Bukola Saraki ba ya Najeriya.

Babu wanda ya isa yayi mana barazana a Majalisa inji Bukola Saraki

Bukola Saraki yace Majalisa ba za ta fasa aikin ta ba

Bukola Saraki yayi tir da harin da aka kai a Majalisar inda yace barazana aka yi wa Damukaradiyya a Najeriya. Yanzu haka dai Saraki yana Amurka inda yake halartar wani taro da babban bankin Duniya da kuma Kungiyar lamuni ta Duniya.

KU KARANTA: Yadda mutane 5 su ka sace sandar girman Majalisa jiya

Saraki ya bayyana cewa dole a hukunta wadanda su kayi wannan aika-aika yayin da yabawa jaruntar Mataimakin sa Ike Ekweremadu na kare Majalisar. Har wa yau Saraki ya yabawa goyon-bayan su da Majalisar Wakilan kasar tayi.

Bayan Bukola Saraki ya samu labarin wannan ta’adi da aka yi lokacin yana wani taro a Amurka yayi maza yayi jawabi ya na mai nuna babu wanda ya isa ya taka Majalisar kasar ya zauna lafiya yana mai kira a dauki tsattsauran mataki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel