Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai

Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai

A jiya ne wasu matasa da ake zargin mamba a majalisar dattijai Sanata Omo Agege ya jagorance su suka sace sandar majalisa.

Matasan sun kutsa kai cikin zauren majalisar a dai-dai lokacin da Sanatan jihar Abiya Theodore Orji ke jawabi kuma basu wai bata lokaci ba suka zare sandar majalisar bayan sun tutture jami'an tsaro dake sanna suka ranta cikin na kare.

Jim kadan bayan afkuwar hargitsin, mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, wanda shine jagorancin zaman majalisar, ya gana da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a fadar gwamnatin tarayya, Aso rock.

Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai

Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai

Da yake bayyana dalilin ziyarar sa, Ekweremadu, ta ce, ya ziyarci Osinbajo ne a matsayin sa na mukaddashin shugaban majalisar dattijai tunda shugaban majalisar, Bukola Saraki, ba ya kasa, domin yiwa Osinbajo cikakken bayanin abinda ya faru a zauren majalisar.

DUBA WANNAN: Duba Jerin sunayen mutanen da suka shiga majalisar dattijai suka sace sandar majalisa

Ekweremadu ya ce, mataimakin shugaban kasar ya jajantawa majalisar bisa abinda ya faru tare da bayyana hakan a matsayin karan tsaye ga doka da kuma nuna raini ga majalisar.

Ekweremadu ya kara da cewar babu wata barazana ko tsoratar wa da zasu hana su gudanar da aikin su na majalisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel