An bayyana sunayen mutane 5 da aka kama bisa zargin satar sandar iko na majalissa

An bayyana sunayen mutane 5 da aka kama bisa zargin satar sandar iko na majalissa

- An bayyana sunayen mutane biyar da suka shiga majlissa suka sace Sandar Girma wanda itace alamar doka a majalissar

- Sanata Ovie Omo-Agege shine ake zargin ya jagoranci mutanen zuwa cikin majalissar wanda hakan ne yasa majalissar ta dakatar dashi

- Mutanen biyar da ake zargi sune Tuoyo Mabiaku, Peter Orede, Blessing Edjeke, Lucky Okomu, sai kuma Prince Enayemo dukansu daga jihar Delta

An bayyana sunayen mutane biyar da suka shiga majlissa suka sace Sandar Girma wanda itace alamar dake nuna doka a majalissar.

Sanata Ovie Omo-Agege shine ake zargin ya jagoranci mutanen zuwa cikin majalissar wanda hakan ne yasa majalissar ta dakatar dashi daga aiki.

An bayyana sunayen mutane 5 da aka kama bisa zargin satar sandar iko na majalissa

An bayyana sunayen mutane 5 da aka kama bisa zargin satar sandar iko na majalissa

Mutanen biyar da ake zargi sune Tuoyo Mabiaku daga Arewacin karamar hukumar warri, Peter Orede daga Kudancin karamar hukumar warri, Blessing Edjeke daga kauyen Abraka dake karamar hukumar Ethiope, Lucky Okomu daga kauyen Oghara dake Yammacin karamar hukumar Ethiope, sai kuma Prince Enayemo daga Kudancin karamar hukumar Ughelli, dukansu daga jihar Delta.

KU KARANTA KUMA: Hukumar ‘Yan Sanda ta gurfanar da ‘yan Shi’a a kotunan dake birnin tarayya

Legit.ng ta ruwaito cewa an goya da masu zanga-zanga ne aka shiga aka sace Sandar Girman daga majalissar, a ranar Laraba 18 ga watan Afirilu 2018, sakamakon cewa masu zanga-zangar magoya bayan Sanatan da aka dakatar ne Omo-Agege.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel