Yadda akayi ‘yan ta’adda 5 suka tsallakewa jami’an tsaro 250 na majalissa kafin suka sace sandar iko

Yadda akayi ‘yan ta’adda 5 suka tsallakewa jami’an tsaro 250 na majalissa kafin suka sace sandar iko

- A kalla akwai jami’an tsaro 250 masu aiki a majalissa lokacinda ‘yan ta’addan biyar suka shiga majalissar suka sato Sandar Girma kuma suka gudu da ita

- Shugaban jami’an tsaro na majalissar ya tabbatarwa manema labarai cewa akwai kimanin jami’ai 500 na tsaro dake aiki a majalissar

- Sun shigo majalissar ne dai dai lokacin da Sanata Ovie Omo-Agege ya iso kofar shiga sai sukace tare dashi suke

A kalla akwai jami’an tsaro 250 masu aiki a majalissa lokacinda ‘yan ta’addan biyar suka shiga majalissar suka sato Sandar Girma kuma suka gudu da ita.

Shugaban jami’an tsaro na majalissar ya tabbatarwa manema labarai na Dailytrust, cewa akwai kimanin jami’ai 500 na tsaro dake aiki a majalissar, wanda rabinsu suna bakin aiki ne a ranakun aiki.

Kuma a cikinsu akwai ‘Yan Sanda masu farin kaya (DSS), sannan akwai ‘Yan Sanda 100, sai jami’an tsaro na gida 300, sai jami’an tsaro na Civil Defence (NSCDC) guda 50, wanda suma ‘Yan Sandan masu farin kaya (DSS) sun kusa 50.

Yadda akayi ‘yan ta’adda 5 suka tsallakewa jami’an tsaro 250 na majalissa kafin suka sace sandar iko

Yadda akayi ‘yan ta’adda 5 suka tsallakewa jami’an tsaro 250 na majalissa kafin suka sace sandar iko

Sun shigo majalissar ne dai dai lokacin da Sanata Ovie Omo-Agege ya iso kofar shiga majalissar da misalign karfe 11.15 na safe, sai sukace tare dashi suke, wanda Sanatan an dakatar dashi a ranar Alhamis data gabata, kuma jiyan ne dama zai halarci zaman majalissar tun da aka dakatar dashi.

KU KARANTA KUMA: Hukumar ‘Yan Sanda ta gurfanar da ‘yan Shi’a a kotunan dake birnin tarayya

Majalissar ta bawa shugaban ‘Yan Sanda masu farin kaya Lawal Daura da kuma na ‘Yan Sanda Ibrahim Idris umurnin kawowa majalissar Sandar cikin awowi 24, an basu umurnin ne da misalin karfe 12.35 na rana, lokacin da mataimaki shugaban majalissar ya kai ziyara bangaren ajiye Sandar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel