Hukumar ‘Yan Sanda ta gurfanar da ‘yan Shi’a a kotunan dake birnin tarayya

Hukumar ‘Yan Sanda ta gurfanar da ‘yan Shi’a a kotunan dake birnin tarayya

- Hukumar ‘Yan Sanda a birnin tarayya ta gurfanar da ‘yan kungiyar Shi’a wadanda ta kama bayan arangamar da tayi dasu a birnin tarayya

- Babban jami’in hukumar na bangaren doka CSP James Idachaba ya tabbatar da cewa 28 cikin ‘yan kungiyar wadanda aka kama sun gurfana a gaban kotun Mpape sai wasu 28 kuma an kai kotun Lugbe

- Wasu 28 kuma an gurfanar dasu a gaban kotun Wuse zone 6 sai sauran cikin mutanen 115 da aka kama an gurfanar dasu a gaban kotun Wuse zone 2

Hukumar ‘Yan Sanda a birnin tarayya ta gurfanar da ‘yan kungiyar Shi’a wadanda ta kama bayan arangamar da tayi ‘yan kungiyar ta Shi’a, a birnin tarayya.

Babban jami’in hukumar na bangaren doka CSP James Idachaba ya tabbatar da cewa 28 cikin ‘yan kungiyar wadanda aka kama sun gurfana a gaban kotun Mpape sai wasu 28 kuma an kai kotun Lugbe.

Hukumar ‘Yan Sanda ta gurfanar da ‘yan Shi’a a kotunan dake birnin tarayya

Hukumar ‘Yan Sanda ta gurfanar da ‘yan Shi’a a kotunan dake birnin tarayya

Wasu 28 kuma an gurfanar dasu a gaban kotun Wuse zone 6 sai sauran cikin mutanen 115 da aka kama a ranar Litinin, an gurfanar dasu a gaban kotun Wuse zone 2.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun saki Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege

Idachaba yace wasu 23 da suka kama bayan 115 da aka fara kamawa an gurfanar dasu a gaban kotun Wuse Zone 2 suma, inda daga nan wasu kotu ta bayar da umurnin a kaisu gidan jarum yara kuma ciki a kaisu gidan tsaro na yara dake jihar Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel