Hargitsi a majalisar dattawa: Jami’an Yansanda sun kwato ‘Sandar Iko’ da ɓarayi suka sace

Hargitsi a majalisar dattawa: Jami’an Yansanda sun kwato ‘Sandar Iko’ da ɓarayi suka sace

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kwato Sanadar Girma ta majalisar dattawa, wanda shi ne alamar iko a majalisar, da idan babu shi, majalisar ba zata zauna ba, kamar yadda Doka ta tanadar.

Premium Times ta ruwaito mataimakin Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Aremu Adeniran ne ya sanar da haka a ranar Laraba 18 ga watan Afrilu, inda yace su gano sandar ne a wani waje, inda barayin suka jefar da shi.

KU KARANTA: Basabamba: Wani Dan majalisa ya koma makaranta don koyar da dalibai Kurame

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa: “Yansanda basu yi wata wata ba suka bi sawun mutanen da suka sace Sandar, ta hanyar gudanar da binciken motoci, tare da bibiyan duk wasu lungunan da miyagun mutane ke zama, da wannan matsin lamba ne barayin suka jefar da sandar a karkashin gadar sama dake gab da kofar shiga Abuja, wanda wani dan kasa na gari ya tsinta, ya kuma sanar da Yansanda.”

Hargitsi a majalisar dattawa: Jami’an Yansanda sun kwato ‘Sandar Iko’ da ɓarayi suka sace

Hargitsi a majalisar dattawa

Sai dai Aremu yace har yanzu basu yi kasa a gwiwa ba, suna nan suna gudanar da bincike na karkashin kasa don tabbatar da sun kamo dukkanin masu hannu cikin wannan abin kunya da aka tafka.

Daga karshe ya gode ma mazauna garin Abuja, musamman direbobi dangane da hadin kan da suka baiwa jami’an Yansanda a yayin da suke gudanar da binciken motoci, don gano sandar.

A ranar Laraba ne dai wasu matasa suka kutsa kai cikin majalisar dattawa, inda suka saci sandar ikon majalisar, tare da arcewa da shi, faruwar hakan ta sanya majalisar baiwa babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris awanni 24 ya nemo musu sandarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel