2019: Kabiru Turaki ne ya dace da kujerar shugabancin kasar nan a jam'iyyar PDP - inji Dattawan Arewa

2019: Kabiru Turaki ne ya dace da kujerar shugabancin kasar nan a jam'iyyar PDP - inji Dattawan Arewa

- Manyan shugabannin jam'iyar ta PDP na arewa maso yamma suna ganin cewa Kabiru Turaki zai iya karawa da jam'iyar APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2019

- Shugabannin jam'iyar ta PDP sun tattauna akan dacewar Kabiru Turaki SAN tsohon ministan kula da harkokin gwamnati akan cewar shi yafi cancanta da tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyar ta PDP. Sun bayyana hakan ne a wani taro da sukayi a Kano

2019: Kabiru Turaki shine ya dace da kujerar shugabancin kasar nan a jam'iyyar PDP - inji Dattawan Arewa

2019: Kabiru Turaki shine ya dace da kujerar shugabancin kasar nan a jam'iyyar PDP - inji Dattawan Arewa

Manyan shugabannin jam'iyar ta PDP na arewa maso yamma suna ganin cewa Kabiru Turaki zai iya karawa da jam'iyar APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Shugabannin jam'iyar ta PDP sun tattauna akan dacewar Kabiru Turaki SAN tsohon ministan kula da harkokin gwamnati akan cewar shi yafi cancanta da tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyar ta PDP. Sun bayyana hakan ne a wani taro da sukayi a Kano.

DUBA WANNAN: Ilimin addinin musulunci ba koma baya bane, haka kuma musulmai ba jahilai bane - Sarkin Musulmai

Shugabannin jam'iyar na jihar Kano sun bayyana ra'ayin sune ta bakin shugabansu Sanata Jibril El mas'ud Doguwa wanda yace a shirye suke wajan goyawa Turaki baya domin neman kujerar shugaban kasa a 2019.

A nasa jawabin tsohon ministan kuma jigo na jam'iyar ta PDP ya bayyana ra'ayinsa akan hakan.

Yace "wannan shine karo na farko da nayi magana akan burina anan jihar kano saboda matsayin jahar a gareni, Kano nada matukar muhimmanci a wajena da kuma aiki na, a domin hakane nake neman goyan bayanku da kuma shawarwarin ku a dangane da takarar tawa.

Ya Kara da cewa yan Nigeria baza su yadda APC taci gaba da mulkar su ba.

Dukkanin wadanda suka halarci taron sun nuna goyon bayansu ga Kabiru Turaki. Sakataren jam'iyar ta PDP Abdullahi Mai Basira ya bayyana cewa yanasa ran jam'iyar tasu ce zata lashe dukkanin zaben da zai gudana a shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel