Gwamnatin tarayya ta karyata jita - jitar kai harin 'Yan Shi'a Abuja

Gwamnatin tarayya ta karyata jita - jitar kai harin 'Yan Shi'a Abuja

- Gwamnatin tarayya tayi watsi da jita-jitar da 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Najeriya wato Shi'a suke yi na cewar zasu kai hari Abuja

- Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ya shaidawa wakilan majalisa, bayan ganawar da wakilan majalisar suka yi a jiya, inda yake bayyana musu cewar bai da masaniya akan jita-jitar

Gwamnatin tarayya ta karyata jita - jitar kai harin 'Yan Shi'a Abuja

Gwamnatin tarayya ta karyata jita - jitar kai harin 'Yan Shi'a Abuja

Gwamnatin tarayya tayi watsi da jita-jitar da 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Najeriya wato Shi'a suke yi na cewar zasu kai hari Abuja.

Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ya shaidawa wakilan majalisa, bayan ganawar da wakilan majalisar suka yi a jiya, inda yake bayyana musu cewar bai da masaniya akan jita-jitar.

DUBA WANNAN: KEDCO nayin asarar miliyan 180 duk wata

Ministan ya bukaci 'yan Najeriya dasu guji yada jita-jita a kafafen sadarwa musamman ma wadanda basu da tushe.

"Saboda haka, dole ne kowa yabi a hankali da abinda yake sakawa a kafar sadarwa, kuma ina mai kara tabbatar muku da cewar duk abinda kuka ji akan kawo harin jita jita ce, kuma muna nan mun kara sanya jami'an tsaro domin kuwa Ministan Abuja yana da masaniya akan zancen saboda abinda ya faru kwanan nan.

"Game da jita - jitar kawo hari kuwa, ina tsammanin wani abu ne da ya kamata mu yi la'akari da inda irin wannan bayanin yake fitowa." Idan akwai wani abu kamar haka, za ku ji shi daga wurin hukuma ne ba daga wurin mutane zauna gari banza ba. "

"Kamar yanda muke yanzu, babu wani abu makamancin haka saboda 'yan sanda suna iya bakin kokarin su wurin ganin sun tsayar da doka a. Na san jama'a sun saurari labaran daren ranar Talata da kuma na ranar Laraba da safe, Kwamishinan 'yan sanda na Abuja ya tabbatar wa da mazauna Abujan cewar babu wani abu da zai faru dasu ko dukiyoyin su".

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel