KEDCO nayin asarar miliyan 180 duk wata

KEDCO nayin asarar miliyan 180 duk wata

- Hukumar kamfanin da yake bada wutar lantarki (KEDCO) ta ce tana asarar naira miliyan 180 a kowanne watan duniya

- Manajan Darakta Kamfanin, Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna, shine ya tabbatar da hakan a wata ganawa da yayi da shugabannin addini dana gargajiya jiya a jihar Kano

KEDCO tana yin asarar miliyan 180 duk wata

KEDCO tana yin asarar miliyan 180 duk wata

Hukumar kamfanin da yake bada wutar lantarki (KEDCO) ta ce tana asarar naira miliyan 180 a kowanne watan duniya.

Manajan Darakta Kamfanin, Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna, shine ya tabbatar da hakan a wata ganawa da yayi da shugabannin addini dana gargajiya jiya a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Neja sunyi nasarar kama manyan barayin nan da suka addabi jihar

Gwamna ya bayyana cewar kamfanin yana kashe naira biliyan 4 kowanne wata wurin sayen wutar lantarkin, amma kuma yana samun naira biliyan 1.8 ko biliyan 1.9.

Ya ce kamfanin ya bukaci dagatai, masu unguwanni da limaman masallatan juma'a na dukkanin kananan hukumomin jihar Kano dasu dinga fadakarwa al'umma akan barnar da suke yi ta wutar a fadin jihar.

Ya kara da cewar banda matsalar ta'addanci da suke samu sai kuma matsalar barayin wuta, inda ya tabbatar da cewar kamfanin yayi wa mutane dubu 500 ne kawai rijista a dukkanin jihohi ukun da kamfanin yake basu wuta sune Kano, Katsina da kuma Jigawa.

"Saboda irin wannan matsalolin ne, da kuma rashin biyan kudin wuta, shine ya tilasta mu neman taimakon malaman addini da shugabannin gargajiya akan su taimaka mana wurin shawo kan al'amarin," inji shi.

Manajan Darakta ya tabbatar cewa, a cikin shekaru biyar da suka wuce, KEDCO ta kashe N8bn a kan samar da wutar lantarki ga jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

A cikin jawabin sa wakilin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi ll, Alhaji Bello Abubakar, ya bukaci KEDCO da ta kirkiro kungiyar hadin guiwa a cikin kowanne gari wanda zai tabbatar da samar da kudaden shiga da kuma hana lalata musu kayan aikin kamfanin.

Har ila yau, Sanusi ya shawarci kamfanin ya ci gaba da fahimtar jama'a don samar da haɗin kai tsakanin su da kamfanin da kuma masu amfani da wutar ta lantarki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel