Ba’a rabu da Bukar ba: Masu garkuwa da mutane sun sace wani Sanata daga majalisun dokoki

Ba’a rabu da Bukar ba: Masu garkuwa da mutane sun sace wani Sanata daga majalisun dokoki

Wani Sanata da ya tsallake rijiya da baya, Sanata Adeola Olamilekan ya bayyana ma jaridar The Cable yadda wasu yan bindiga suka dira farfajiyar majalisun dokokin Najeriya, suka yi awon gaba da shi a ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu.

Sanatan ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa “Allah ya tseratar dani daga hannun masu garkuwa da mutane da suka sace ni a cikin wata mota, inda suka yi kokarin ficewa da ni ta kofar fadar shugaban kasa, amma a daidai sashin majalisar wakilai na diro daga motar na tsere.”

KU KARANTA: Yawanci matasan Najeriya basu son karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando – Buhari daga Landan

Wani hadimin Sanatan yana bayyana cewar yan bindigar sun sace Maigidan nasa, amma Allah ya tseratar da shi, sai da yace lamarin baya rasa nasaba da kiran da yayi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami shuwagabannin hukumomin tsaron Najeriya saboda gazawarsu wajen tabbatar da tsaro a Najeriya.

Ba’a rabu da Bukar ba: Masu garkuwa da mutane sun sace wani Sanata daga majalisun dokoki

Sanata Adeola

Hadimin ya tabbatar ma majiyar Legit.ng cewar a yanzu haka Sanatan na fama da targade a kafarsa, wanda ya sameta a lokacin da yayi kokarin dirowa daga motar yan bindigan, sai dai yace yana samun sauki.

A yayin zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, Sanata Adeola yayi kira da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige shuwagabannin tsaro sakamakon rashin tabuka komai, musamman a jihar Nassarawa, inda rikicin makiyaya da manoma yayi kamari.

Ba’a rabu da Bukar ba: Masu garkuwa da mutane sun sace wani Sanata daga majalisun dokoki

Bayaninsa

Shima a nasa bangaren, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar ya tabbatar da yunkurin satar Sanatan, inda yace Sanatoci biyu kenan aka yi kokarin sacewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel