Yanzu-yanzu: APC ta bayyana ranan taron gangaminta da zaben sabbin shugabanni

Yanzu-yanzu: APC ta bayyana ranan taron gangaminta da zaben sabbin shugabanni

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta bayyana ranan da za ta gudanar da taron gangaminta na kasa ga baki daya da kuma zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

Game da jadawalin da sakataren gudanarwan jam'iyyar, Osita Izunaso, ya saki, za'a gudanar da taron gangami ranan 14 ga watan Mayu, 2018.

Za'a gudanar da na unguwanni ranan 2 ga watan Mayu, na kananan hukumomi ranan 5 ga watan Mayu, sannan na jihohi ranan 9 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Jerin sunayen matasan da suka kai hari majalisar dattijai suka dauke sandar majalisa

Gabanin yau jam'iyyar ta yi kira ga hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta halarto domin tayasu gudanar da wadannan zabubbuka.

Wannan na kunshe cikin wasikar da sakataren jam'iyyar, Mai Mala Buni, ya rubutawa hukumar.

Za ku tuna cewa sabanin yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada na gudanar da zabe da taron gangami bayan ko wani shekara 2, jam'iyyar APC bata gudanar da taron gangamin ba tun shekarar 2014.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel