Kasar Ingila zata antayo biliyoyin kudi ga talakawan Najeriya, ji me take so ayi dasu

Kasar Ingila zata antayo biliyoyin kudi ga talakawan Najeriya, ji me take so ayi dasu

- "Kwayar cutar zazzabin cizon sauro da sauro sun kangare"

- UK tace zata fito da Sabon shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da kimanin miliyan £50 wanda zai kai har 2024

- UK tace zata samar da miliyan £9.2 don sabon binciken samar da sabon triple artemisinin combination

Kasar Ingila zata antayo biliyoyin kudi ga talakawan Najeriya, ji me take so ayi dasu

Kasar Ingila zata antayo biliyoyin kudi ga talakawan Najeriya, ji me take so ayi dasu

A wani bayani da kungiyar taimakon kai da kai mai suna "Ready to beat malaria" ta saki, tacece Gwamnatin Birtaniya watau UK, ta kara tabbatar da cewa zata kashe miliyan £500 duk shekara akan cutar zazzabin cizon sauro tun daga 2020-21.

A zancen an kara cewa UK zata sanar da karin miliyan £100. Tallafin kudin na daga cikin kokarin Birtaniya don cigaban yaki da zazzabin cizon sauro.

Za a sanar da wadannan zantukan ne a taron da za'ayi na yaki da zazzabin cizon sauro a Landan 2018,wanda Gwamnatin UK da hadin guiwar shugaban kasar Rwanda da Swaziland suka dau nauyi.

Ance shuwagabannin kasashe 15 da gwamnatoci daga Commonwealth zasu halarta, tare da ministoci da shuwagabannin daga duniyar kasuwanci, kimiyya da kuma kungiyoyin kasashen duniya.

Zancen yace makaman yaki da cutar zazzabin cizon sauro sun hada da raga da magungunan sauro yanzu basu amfani.

"Gwamnatin UK tana alfaharin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, inda muka ga ragewar mutuwa da kashi sittin cikin dari kuma an tseratar da rayuka miliyan 7 tun 2000"

DUBA WANNAN: An saki bidiyo da ba lallai yayi wa Buhari ko APC dadi ba

"Mun bada gudummawar mu don ganin cigaban ta hanyar ware dala miliyan 500 duk shekara har nan da shekaru uku, domin samar da sababbin magunguna da fasahohi da kuma samar da mafita ga masu cutar."

"Amma har yau bamu kammala aikin ba saboda akwai miliyoyin rayuka da basu tsira ba. Cutar tana daukan rayukan kananan yara a kowanne lokaci" saboda haka ne nake jagorantar Commonwealth don yaki da cutar har zuwa 2023" inji Theresa May.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel